14 Oktoba 2021 - 11:48
​Putin: ‘Yan Ta’addan Daesh Na Ci Gaba Da Yin Turuwa Zuwa Kasar Afghanistan

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa; 'yan ta'adda daga Iraki da Siriya suna tururuwa zuwa kasar Afghanistan," kuma suna kawo barazana ta tsaro ga iyakokin kasashe makwabtan kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Putin ya ce, "Dangane da wannan batu, yana da mahimmanci a ko yaushe a sanya ido kan halin da ake ciki a kan iyakar kasar Afghanistan, kuma a yi shirin tunkarar 'yan bindigar, kuma saboda wannan yakamata jami'an tsaro da hukumomin tsaro su hada karfi da karfe wajen gudanar da ayyukansu ta fuskar tsaro.

Haka nan kuma in ya bayyana halin da ake ciki a Afganistan bayan janyewar sojojin Amurka da cewa "abu ne mai wahala da sarkakiya matuka, wanda hakan yana da alaka ne da ayyukan kungiyar ‘yan ta’adda ta daesh da ke a matsayin babbar barazana a halin yanzu a kasar Afghanistan.

Putin ya ce, " a taron kungiyar CSTO, da Kungiyar Hadin Kan Shanghai a watan Satumban da ya gabata, an tattauna batutuwa da ke haifar da barazanar tsaro ga kasashen yankin Tsakiyar Asiya, yankin Caucasus da sauran yankuna.

Haka nan kuma ya ce tabbas za a tattauna wannan batu a taron kasashe makwabtan kasar Afghanistan, wanda za a gudanar nan bad a jimawa ba.

342/